News
Gwamnatin jihar Niger ta rushe wani ofishin ‘yan sanda da ke birnin Minna
Gwamnatin jihar Niger ta rushe wani ofishin ‘yan sanda da ke birnin Minna babban birnin jihar
Gwamnan jihar Umar Ɓago shine ta ba da umarnin rushe ofishin ‘yan sandan na unguwar Chanchaga da ke birnin Minna.
An Kama Karin Mutane 57 Da Sace Kayyaki A Wuraren Da Gwamnatin Kano Ke Aikin Rusau
A cewar mai bai wa gwamnan jihar Niger shawara kan harkokin yaɗa labarai na zamani, Abdulberqy Ebbo, ya ce ofishin ‘yan sandan an gina shi ne ba bisa ka’ida ba akan layin bututun ruwa.
Gaskiya Ta Fi Kwabo ta ruwaito cewa, yayin da ya ke gabatar da jawabin a ranar rantsar da shi, gwamna Umar Bago ya sha alwashin rushe ofishin ‘yan sandan wanda ya ce yana daƙile yunƙurin gwamnati na samar da tsaftataccen ruwan sha ga al’ummar birnin Minna.
Advertisements
