News
Tinubu ya sake ganawa da Kwankwaso a Villa
Shugaba Bola Tinubu na ganawa da jagoran jam’iyyar NNPP na ƙasa, Rabiu Musa Kwankwaso a fadar shugaban ƙasa, Abuja.
Kwankwaso ne dan takarar shugaban kasa na farko a zaben 2023 mai cike da rudani da ya ziyarci Tinubu a fadar Aso Rock Villa.
Idan da Kwankwaso ya Bari na hadu da shi sai na wankeshi da mari: Inji tsohon gwamna Ganduje
A tuna cewa a ranar 16 ga Mayu, Tinubu da Kwankwaso sun gana a Faransa don tattaunawar zaman lafiya.
Rahotanni sun ce Mista Tinubu ya nemi Kwankwaso da ya tuntubi abokan siyasarsa kan bukatar yin aiki tare.
An ce shugaban kasar da Kwankwaso sun amince da ci gaba da ganawa a gaba.
Advertisements
