Connect with us

News

Gwamnatin Kano Ta Kammala Shirye-Shiryen Yin Auren Zawarawa 1500

Published

on

FB IMG 1773953278977 750x430

Gwamnatin jihar Kano ta ce ta kammala shirye-shiryen yin auren zawarawa ga mutum 1,500 karkashin shirin tallafin jin ƙai da ta kira “Auren Gata”.

Mataimakin babban kwamandan Hukumar Hisbah ta jihar, Dr. Mujahideen Aminudeen, ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN a Kano.

Advertisement

Italiya Ta Yi Watsi Da Tayin Trump Na Neman Ta Maye Gurbin Iran A Gasar Cin Kofin Duniya Ta 2026

Ya ce shirin na daga cikin kokarin gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf na tallafa wa marasa karfi a cikin al’umma, musamman wajen saukaka matsalolin aure.

Advertisement

Ya kara da cewa an yanke shawarar kara fadada shirin ne sakamakon nasarorin da aka samu a shirye-shiryen baya, wanda ya karfafa gwiwar gwamnati wajen ci gaba da zuba jari a cikinsa.

Aminudeen ya ce gwamnan ya bayar da umarnin kammala dukkan shirye-shiryen kafin karshen watan Mayu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending