Connect with us

News

Kotu Ta Ɗaure Matashin Da Ya Kashe Mahaifinsa Ta Hanyar Zuba Masa Guba A Cikin Abinci

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Kotun majistare dake zama a Minna jihar Neja ta daure wani matashi mai shekara 24 Mizanmil Abubakar bisa laifin kashe mahaifinsa ta hanyar zuba masa guba a cikin Abinci.

Advertisement

Premium Times ta ruwaito cewa sashen dake gurfanar da masu aikata laifuka irin haka na rundunar ‘yan sandan jihar ta shigar da karar.

DA DUMI DUMI: Kungiyar Likitoci Sun Fara Yajin Aikin Gargadi A Najeriya 

Rundunar ta ce ta samu bayanin abin da Abubakar ya aikata bayan karar da wani Abubakar Abdullahi dake zama a Sauka Kahuta ya shigar ranar 29 ga Yuni.

Advertisement

Bisa ga karan Abdullahi ya ce Abubakar ya kashe mahaifinsa Abubakar Adawa a gidan su dake Model City a Barikin Saleh ranar 28 ga Yuni da karfe 12 na rana.

Abdullahi ya ce a ranar duk an fita an bar Abubakar da mahaifinsa su kadai a gida, bayan sun dawo gida sai ba su ga mahaifin ba, da suka tambayi ina ya tafi sai Abubakar ya ce bai san inda ya ke ba.

Advertisement

“Ganin haka ya sa aka sanarsa da ‘yan sanda inda bayan sun gudanar da bincike suka tsinci gawar mahaifin a cikin wani rami an yi gunduwa-gunduwa da shi.

“Bayan an tsinci gawar sai Abubakar ya bayyana cewa ya zuba maganin bera ne a cikin abinci sannan ya ba mahaifinsa abinci ya ci don ya mutu.

Advertisement

“Abubakar ya ce ko da mahaifin ya ci abincin bai mutu ba amma bai iya ko motsi da jikinsa, daga nan sai ya ɗauko fatanya dike shi da shi, har sai da ya mutu, sannan ya daddatsa jikinsa, ya yi gunduwa-gunduwa da shi ya turbuda a rami ya rufe.

“Matashi ya ce ya kashe mahaifinsa ne saboda yadda yake yawan kai karan sa wajen ‘yan banga.

Advertisement

A kotun Abubakar ya musanta aikata laifin da ake zargin sa da shi.

Dan sandan da ya shigar da karar Bello Beji ya ce za su kai karar laifin da Abubakar ya aikata ma’aikatar shari’a.

Advertisement

Alkaline kotun Ummulkhatum Mohammed ta yanke hukuncin daure Abubakar a gidan gyaran hali sannan za a ci gaba da shari’a ranar 18 ga Satumba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending