News
DA DUMI DUMI: Kungiyar Likitoci Sun Fara Yajin Aikin Gargadi A Najeriya
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Kungiyar Likitoci ta Najeriya NARD ta fara yajin aikin gargadi na kwanaki bakwai a kan sace Dr Ganiyat Popoola na sashin kula da ido ta kasa a jihar Kaduna da aka yi garkuwa da shi kusan watanni takwas da suka gabata.
Shugaban Kungiyar NARD, Dr Dele Abdullahi, shine ya bayyana hakan a ranar Lahadi, ya ce za a fara yajin aikin ne a ranar Litinin 26 ga watan Agusta, 2024 da karfe 12 na safe.
Abdullahi ya ce an yanke shawarar ne a yayin taron majalisar zartarwar Kungiyar ta kasa.
Ya ce, “Yajin aikin ya fara ne da tsakar daren yau. Kwanaki bakwai ne, yajin gargadi ne.
A ranar 27 ga Disamba, 2023,ne a kayi garkuwa da Popoola, mai rijista a sashen kula da lafiyar ido a cibiyar kula da ido ta kasa, Kaduna, tare da mijinta da kuma dan uwanta.
Yayin da aka saki mijinta a watan Maris, Popoola da dan uwanta suna ci gaba da tsare.
Membobin Kungiyar NARD sza suyi zanga-zanga a dukkan manyan asibitocin kasar don neman a sako Dr Popoola.
-
News3 days agoWasu Ƴan Daba Sun Kai Farmaki Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Center Dake Kano
-
News6 days agoWasu Fusatattun Matasa Sun Ƙona Mutum Uku Har lahira A Filato
-
News5 days agoAbin Takaici Ne A Kyale Mata Su Cire Wandunan Da Aka Basu Akan Titi Suna Dagawa A Cikin Al’ummar Da Ke Alfahari Da Kunya Da Addini
