News
Likitoci Sun Tsunduma Yajin Aiki A Najeriya
Ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa ta Najeriya NARD, ta sanar da shirin ta na tsunduma yajin aikin sai Baba ta gani a duk faɗin ƙasar, daga ranar Talata 7 ga Afrilu, 2026.
Sakataren Janar na kungiyar, Dakta Shuaibu Ibrahim, ne ya bayyana hakan bayan wani taron gaggawa na kwamitin zartarwa na Ƙungiyar (NEC) da aka gudanar ta yanar gizo a ranar Asabar.
Aƙalla Mutane 11 Ne Suka Mutu Sannan Aka Ƙona Gidaje 50, Bayan Ɓarkewar Rikici A Nasarawa
Ya ce matakin ya biyo bayan kudurin gwamnatin tarayya na dakatar da aiwatar da sabon tsarin karin alawus na kwarewar likitoci, wanda aka fi sani da Professional Allowance Table (PAT).
Dakta Ibrahim ya bayyana wannan mataki a matsayin abin takaici, yana mai cewa ya sake jefa bangaren lafiya cikin wani sabon rikici.
A cewarsa, “Bayan tattaunawa mai zurfi, kwamitin zartarwa ya amince da fara cikakken yajin aiki daga karfe 12 na tsakar dare ranar 7 ga Afrilu, 2026.”
Tun da farko dai, an cimma yarjejeniya tsakanin kungiyar da gwamnatin tarayya a shekarar 2025, bayan wani dogon yajin aiki, inda aka amince da sabon tsarin alawus domin inganta jin dadin likitocin horaswa.
Sabon tsarin ya hada da karin alawus na aikin kira, aikin juyin aiki, aiki a yankunan karkara, da kuma ayyukan da ba na kai tsaye ba.
Sai dai kungiyar ta zargi gwamnati da yunkurin dakatar da aiwatar da wannan tsari daga watan Afrilu, duk da cewa an tsara fara aiwatar da shi tun daga farkon shekarar 2026.
Kungiyar NARD ta ce wannan mataki ya sabawa yarjejeniyar da aka cimma, tare da karya amincewa tsakanin bangarorin biyu.
Daga cikin bukatun da kungiyar ta gabatar akwai soke wannan mataki nan take, biyan dukkan basussukan alawus, da kuma kammala biyan kudaden horas da likitoci na shekarar 2026.
Haka kuma, kungiyar ta bukaci mambobinta da su ci gaba da hada kai domin ganin an kai ga cimma matsaya.
