News
Aƙalla Mutane 11 Ne Suka Mutu Sannan Aka Ƙona Gidaje 50, Bayan Ɓarkewar Rikici A Nasarawa
Rundunar ƴansandan jihar Nasarawa da ke tsakiyar Najeriya, ta tabbatar da mutuwar mutane 11 da kuma ƙona gidaje 50, sanadiyar ɓarkewar rikici tsakanin al’ummar Akyawa da Udege Kasa da aka samu a jihar.
A cikin sanarwar da kakakin rundunar ƴansandan jihar SP Ramhan Nansel ya fitar a yau, ya bayyana cewar adadin mutanen da aka kashe ya sanya kwamishinan ƴansandan jihar Shetima Jauro Mohammed, ziyartar yankin da abin ya faru don maido da zaman lafiya.
Jami’an Ƴansanda Sun Sun Kama Mata Biyu Bisa Zargin Sace Jariri A Nasarawa
A lokacin ziyarar, CP Shetima ya bayyana damuwarsa kan yadda lamarin ya faru, inda ya jajantawa iyalan waɗanda abin ya shafa, tare da tabbatar musu da aniyarsu na ganin anyi musu adalci.
Kwamishinan ya kuma bada umarnin gudanar da bincike don kamo waɗanda ake zargi da aikata laifin, wanda rahotanni suka nuna cewa a ranar Juma’ar data gabata ne aka samu tashin rikicin.
