Connect with us

News

Jami’an Ƴansanda Sun Sun Kama Mata Biyu Bisa Zargin Sace Jariri A Nasarawa ‎

Published

on

FB IMG 1775231409632
Advertisements
WhatsApp Image 2026 10 20 at 1.48.05 PM

Rundunar ‘yan sandan Jihar Nasarawa ta sanar da ceto wani jariri namiji mai kwanaki uku da aka sace a yankin Mararaba, yayin da ta kama mata biyu da ake zargi da hannu a lamarin.

‎Mai magana da yawun rundunar, Ramhan Nansel, ya ce mahaifiyar jaririn, Aisha Bada, mai shekaru 19, ce ta kai rahoton sace jaririn bayan wasu mutane da ba a san ko su wanene ba sun shiga inda take tare da jaririn suka dauke shi.

‎An Tura Ƙarin Dakarun Soji 850 Domin Tabbatar Da Tsaro A Filato

‎‘Yan sanda sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar 28 ga watan Maris, a wani gini da ba a kammala ba da ke unguwar Unguwan Bako a Mararaba, cikin karamar hukumar Karu, inda mahaifiyar ke barci tare da jaririn.

‎Bayan samun rahoton, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Shetima Mohammed, ya umarci a fara bincike cikin gaggawa. Daga bisani, jami’an tsaro sun gudanar da samame bisa sahihan bayanan sirri, wanda ya kai ga kama wasu mata biyu, Furera Abdulrahman da Sadiya Abdullahi.

‎A cewar ‘yan sanda, matan sun amsa laifin da ake zarginsu da shi, tare da bayyana cewa suna da wani abokin aikata laifin da har yanzu ake naima , inda ake ci gaba da kokarin cafke shi.

Advertisement

‎An kai jaririn asibiti domin duba lafiyarsa, inda aka tabbatar yana cikin koshin lafiya kafin a mika shi ga iyayensa.

 

 

DAILY REPORTS

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending