Connect with us

News

Likitoci Sun Tsunduma Yajin Aiki Kan Korar Ma’aikata 127

Published

on

Kungiyar Ƙananan Likitoci ta Najeriya (NARD), reshen Babban Birnin Tarayya Abuja, ta ce za ta shiga yajin aikin gargadi na kwanaki uku daga yau Talata, domin nuna rashin jin daɗinta kan korar ma’aikatan lafiya 127 da hukumar kula da ma’aikatan Abuja (FCTA) ta yi.

Kungiyar Likitoci ta yanke shawarar shiga yajin aikin ne bayan wani taron gaggawa da ta gudanar a Asibitin Asokoro a ranar Litinin, kamar yanda Jaridar DAILY TRUST ta ruwaito.

Advertisement

An Kashe Sama Da Mutane 1,700 A Rikicin Iyakoki Da Muhalli A Najeriya — RAHOTO 

Shugaban ƙungiyar, Dr George Ebong, ya bayyana matakin da hukumar FCTA ta dauka a matsayin “maras tushe kuma rashin imani.” Ya ce dole ne a gaggauta dawo da ma’aikatan bakin aiki tare da biyansu albashin watan Afrilu da aka dakatar.

“Wannan korar ba ta da wani dalili na kwarai kuma tana nuna yadda ake raina ma’aikatan lafiya. Ba za mu yarda da hakan ba,” in ji Dr. Ebong.

Advertisement

Ya kuma bukaci shugaban hukumar kula da ma’aikatan Abuja, Emeka Ezeh, da ya sauka daga mukaminsa saboda yadda aka tafiyar da al’amarin.

Kungiyar ta yi gargaɗi cewa idan Ministan Abuja, Nyesom Wike, bai dauki matakin da ya dace cikin kwanaki uku ba, to za su shiga yajin aikin sai baba ta gani, wanda hakan na iya haddasa durƙushewar harkokin lafiya a babban birnin tarayya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending