Connect with us

News

‎Kungiyar Likitoci Za Ta Sake Tsunduma Yajin Aiki Daga Ranar 12 Ga Janairu

Published

on

doctors (1)
Spread the love

‎Kungiyar Likitoci Masu Neman Kwarewa ta Ƙasa (NARD) ta sanar da cewa za ta sake tsunduma cikin yajin aikin dindindin gaba ɗaya daga ranar Litinin 12 ga Janairu, 2026, idan har gwamnatin tarayya ba ta aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma da ita ba.

‎Kungiyar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da shugabanta, Dr Mohammad Suleiman, ya fitar a ranar Asabar, bayan kammala taron gaggawa na kwamitin zartarwarta na Kungiyar.

Dakarun Soji Sun Gano Albarusai Masu Yawa A Cikin Kwata A Maiduguri

‎A cewar NARD, matakin komawa yajin aikin ya biyo bayan gazawar gwamnatin tarayya da Ma’aikatar Lafiya wajen cika alkawuran da ke cikin yarjejeniyar fahimta da aka rattaba hannu a kanta, bayan dakatar da yajin aikin da kungiyar ta yi a baya.

‎Kungiyar ta ce a makon da ya gabata ta riga ta yi gargadi cewa ayyukan asibitoci a faɗin Najeriya na iya fuskantar tsaiko, idan ba a samu matsaya tsakanin ɓangarorin ba.

Advertisement

‎Sanarwar ta ƙara da cewa yajin aikin, wanda aka sanya masa taken “No Implementation, No Going Back”, zai fara aiki ne da misalin ƙarfe 12 na dare a ranar 12 ga Janairu, 2026.

‎NARD ta ce ta yanke wannan shawara ne domin ƙara matsin lamba ga gwamnati ta aiwatar da buƙatun likitocin da aka amince da su tun bayan dakatar da yajin aikin da ya gabata.

‎Har ila yau, kungiyar ta bayyana shirin gudanar da zanga-zanga a asibitoci a faɗin ƙasar nan daga ranar 12 zuwa 16 ga Janairu, tare da shirya tarukan manema labarai a cibiyoyi 91 na kungiyar.

‎A cewar NARD, zanga-zangar za ta fara ne daga matakin cibiyoyi, kafin daga bisani a faɗaɗa ta zuwa matakin yanki da kuma na ƙasa baki ɗaya.

Advertisement

‎Kungiyar ta jaddada cewa ba za ta sake dakatar da yajin aikin ba, sai dai idan gwamnatin tarayya ta aiwatar da dukkan buƙatun da aka cimma yarjejeniya a kansu gaba ɗaya.

‎A ranar 29 ga Nuwamba, NARD ta dakatar da yajin aikinta na kwanaki 29, bayan cimma yarjejeniya da gwamnati, wadda ta yi alkawarin cika buƙatun likitocin cikin makonni huɗu.

‎Daga cikin buƙatun kungiyar akwai: biyan basussukan albashi da na ƙarin girma,

‎cikakken aiwatar da jadawalin alawus na ƙwararru,

Advertisement

‎warware jinkirin albashin house officers,

‎sake dawo da alawus na ƙwarewa,

‎da kuma kammala tattaunawar yarjejeniyar albashi ta gama-gari.

‎Kungiyar ta ce ta bayar da wa’adin mako guda domin bai wa shugabannin cibiyoyinta damar kammala tattaunawa da manema labarai, tare da sanar da shugabannin asibitoci da hukumomin tsaro game da matakin da ta ɗauka.

Advertisement

 

 

SOLACEBASE

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *