Connect with us

News

Dakarun Soji Sun Kama Mutane Biyu Da Makamai A Jos

Published

on

WhatsApp Image 2026 04 05 at 1.58.17 AM

Rundunar sojojin Najeriya ta ce ta kama wasu mutane biyu dauke da makamai a garin Jos, babban birnin jihar Plateau, yayin da ta kaddamar da wani shiri na tsauraran binciken ababen hawa a fadin birnin.

A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Asabar, jami’in yada labarai na rundunar hadin gwiwa ta Operation Enduring Peace, Kyaftin Chinonso Polycarp Oteh, ya bayyana cewa an fara aikin ne tun ranar Juma’a, a wani bangare na kokarin dawo da cikakken zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyi a jihar.

Likitoci Sun Tsunduma Yajin Aiki A Najeriya

Sanarwar ta ce matakin ya riga ya fara haifar da sakamako mai kyau, inda sojojin suka kama wadanda ake zargin tare da kwato makamai, ciki har da wata bindigar AK-47 da aka kera ba bisa ka’ida ba, harsasai guda hudu masu girman 7.62mm, da kuma wata bindigar pump action.

An gudanar da samamen ne a wasu muhimman wurare da hanyoyin wucewa a cikin birnin Jos, da suka hada da Jos North da Jos South, Dadinkowa, mahadar Old Airport, Tudun Wada da kuma unguwar gidajen Low-cost.

 

Advertisement

DAILY POST

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending