News
Shugaban INEC Na Neman Yi Wa Hukuncin Kotu Hawan Ƙawara — ADC
Jam’iyyar ADC ta zargi shugaban Hukumar Zabe ta Kasa, Joash Amupitan, da raina kotu, tare da jaddada cewa za ta ci gaba da gudanar da tarukanta na jam’iyya da babban taron kasa kamar yadda ta tsara.
A cikin wata sanarwa da kakakin jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, ya fitar a ranar Juma’a, ADC ta yi watsi da kalaman shugaban INEC da ya yi a wata hira da tashar Arise Television, inda ya gargadi jam’iyyar da cewa gudanar da irin wadannan taruka na iya saba wa umarnin kotu da ake da shi a halin yanzu.
Dakarun Soji Sun Kama Mutane Biyu Da Makamai A Jos
Jam’iyyar ta bayyana matsayar INEC a matsayin “karkatar da gaskiya da gangan” dangane da umarnin Kotun Daukaka Kara na ci gaba da riƙe halin da ake ciki (status quo), tana mai cewa hukumar ta wuce iyakar aikinta na sa ido.
ADC ta ce za ta ci gaba da shirinta na gudanar da tarukanta da babban taron kasa, tana mai jaddada cewa babu wata kotu da ta dakatar da wadannan ayyuka.
“Hakkin ADC na shirya taruka da gudanar da babban taron kasa yana cikin kundin tsarin mulki, kuma babu wata kotu da ta haramta hakan,” in ji sanarwar.
Rikici kan fassarar umarnin kotu
Jam’iyyar ta zargi shugaban INEC da kuskuren amfani da ka’idar status quo ante bellum, tana mai cewa umarnin kotu ba ya nufin dakatar da harkokin cikin gida na jam’iyya.
A cewarta, irin wannan umarni na nufin hana duk wani mataki da zai iya sauya yanayin shari’ar gaba ɗaya, ba wai ya dakatar da ayyukan jam’iyya ba.
ADC ta kuma jaddada cewa fassara abin da ake nufi da “status quo” aiki ne na kotu kadai, ba na wata hukuma kamar INEC ba.
Matsayar ADC kan rawar INEC
Jam’iyyar ta ce babu wani umarni da ya hana ta gudanar da taruka, tana mai cewa tsarin dimokuraɗiyya a cikin jam’iyya bai kamata ya tsaya ba sai idan kotu ta bayar da takamaiman umarni.
Haka kuma, ADC ta yi watsi da matsayar INEC cewa ba za ta sa ido kan tarukanta ba saboda shari’ar da ke gaban kotu, tana mai cewa hakan ya nuna rashin fahimtar aikin hukumar.
A cewar jam’iyyar, rashin halartar INEC a irin wadannan taruka ba ya sa su zama ba su da inganci, domin aikin hukumar na sa ido yana fara ne bayan an sanar da ita yadda doka ta tanada.
“Ta hanyar haɗa aikin sa ido da sahihancin taruka, INEC na nuna kamar ta fi doka karfi,” in ji ADC.
Bayan fage
Rikicin tsakanin INEC da ADC ya samo asali ne bayan hukumar ta sanar da cewa ba za ta amince da kowanne bangare na shugabancin jam’iyyar ba har sai Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke hukunci kan karar da ke gabanta.
Rikicin shugabanci ya taso ne bayan tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa, Nafiu Bala, ya kalubalanci nadin David Mark a matsayin shugaban jam’iyyar.
A cewar Bala, shi ne ya kamata ya gaji shugabancin jam’iyyar bayan murabus din tsohon shugaba, Ralph Nwosu.
A ranar 18 ga Satumba 2025, bangaren Mark ya shigar da kara a Kotun Daukaka Kara, amma an yi watsi da ita a ranar 12 ga Maris. Bayan haka, kotun ta umarci dukkan bangarorin da su ci gaba da riƙe halin da ake ciki (status quo ante bellum) har sai kotun ƙasa ta yanke hukunci kan ainihin shari’ar.
Bisa wannan umarni ne INEC ta ce ba za ta yi mu’amala da kowanne bangare ba har sai an kammala shari’ar, sai dai ADC ta soki wannan fassara tana mai cewa ba ta da tushe a doka.
-
News6 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News2 days ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News7 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
