Connect with us

News

Uba Ya Rasa Ransa Yayin Ƙoƙarin Ceto ‘Yarsa Da Ta Faɗa Rijiya A Kano

Published

on

Rijiya

Wani mutum mai suna Abubakar Abdullahi, mai shekaru 45, da ‘yarsa Fiddausi, mai shekaru 15, sun rasu bayan sun faɗa cikin wata rijiya a garin ‘Yancibi da ke Ƙaramar Hukumar Tsanyawa a Jihar Kano.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da yammacin ranar Talata, lokacin da Fiddausi ta faɗa cikin rijiyar. Mahaifinta, Abubakar Abdullahi, ya shiga rijiyar ne domin ceto ta, amma abin takaici shi ma ya makale a ciki.

Gwamnan Kano Ya Kaddamar Da Kwamitin Yaƙi Da Miyagun Ƙwayoyi, Ya Sa Hannu Kan Dokar Hana Daba A Kano

Kakakin Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Yusuf Abdullahi, ya bayyana cewa jami’an hukumar sun yi ƙoƙarin ceto mutanen biyu a daren ranar, sai dai duhun rijiyar da kuma mawuyacin yanayin aikin sun hana nasarar ceto su cikin lokaci.

Ya ce da safiyar ranar Laraba ne aka sake komawa wurin da tawagar ceto, inda aka samu nasarar fito da su daga rijiyar bayan dogon ƙoƙari, amma tuni sun rasa hayyacinsu. Daga bisani likitoci suka tabbatar da rasuwarsu.

Kakakin hukumar ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan da al’ummar garin ‘Yancibi, tare da jan hankalin jama’a da su guji shiga rijiyoyi ba tare da ingantattun kayan kariya da na aikin ceto ba, domin kauce wa irin waɗannan munanan haɗurra.

Advertisement

Lamarin ya jefa al’ummar yankin cikin alhini, yayin da ake jimamin rasuwar uban da ya sadaukar da ransa wajen ƙoƙarin ceto ‘yarsa.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending