Connect with us

News

Ƙungiyar Ƙwadago ta nemi a ƙara gejin mafi ƙanƙatar albashi daga Naira 30,000 zuwa Naira miliyan 1

Published

on

DAGA YASIR KABIRU BASIRU 

Yayin da ‘yan Najeriya ke fama da raɗaɗin tsadar rayuwar da ta kai har an fara yi wa yunwa zanga-zangar fito-na-fito a wasu sassan ƙasar nan, Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago ta NLC, Joe Ajaero, ya bayyana cewa mai yiwuwa ƙungiyar ta nemi Gwamnatin Najeriya ta yi ƙarin mafi ƙanƙantar albashi daga Naira 30,000 ya koma daga daga Naira miliyan 1 zuwa sama.

Advertisement

Ajaero ya bayyana hakan a ranar Lahadi, yayin da ake tattaunawa da shi a gidan talabijin na Arise dangane da matsalolin da ake fuskanta da kuma halin tsadar rayuwar da ake fama a Najeriya.

Bankin IMF ya shawarci Najeriya ta ƙara cire tallafin fetur da tallafin kuɗin lantarki

Ya ce neman wannan adadin albashi ya zama tilas idan aka yi la’akari da yadda kayan abinci da sauran kayan tafiyar da rayuwar yau da kullum ke ƙara tashin farashi a kullum.

Advertisement

“Naira miliyan 1 a matsayin mafi ƙanƙantar albashi ba aibu ba ne, idan aka yi la’akari da yadda farashin kayan abinci da sauran kayayyaki ke ƙara tashi. Sai kuma a yi duba dangane da yadda a kullum darajar Naira ke faɗuwa.

“Don haka idan Naira ta ci gaba da faɗuwar darajar da ta ke yi, kuma farashin kayan abinci da kayan masarufi da kayan buƙatun yau da kullum na rayuwar jama’a suka ci gaba da tashin farashi, to lallai za mu nemi a biya ma’aikacin Najeriya Naira miliyan 1 a matsayin mafi ƙanƙantar albashi,” cewar Ajaero.

Advertisement

“Za ku tuna cewa yayin da muke neman a biya mu Naira 200,000 matsayin albashi mafi ƙaranci, lokacin ai Naira 800 ake sayar da Dala 1, ko Naira 900. To amma a yanzu Dala 1 ta haura Naira 1,400.”

Ajaero daga nan ya riƙa lissafo farashin kayan abinci a halin da ake ciki yanzu, ya na kwatanta su da ɗan albashin da ake bai wa ma’aikaci, wanda a yanzu ya ce kuɗin ba su fi a sayi abinci cikin cokali ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending