News
Tsadar Rayuwa: Yadda aka wawushe wa ɗan kasuwa kayan ‘sama da miliyan 100‘ a Abuja
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
A baya-bayan nan ne wasu mutane da ake jin sun kai 300 suka fasa wani rumbun ajiye kayyaki a unguwar Karmo da ke wajen Abuja, babban birnin Najeriya inda suka wawashe shi.
Rahotanni na nuni da cewa Rumbun, a cewar Murtala Ibrahim, ɗan kasuwa a yankin na Karmo, yana cike da kayan da kuɗinsu ya kai naira miliyan ɗari biyu da goma.
Tsadar Rayuwa: Garin kwaki ma nema ya ke ya gagari talakawan Najeriya
Ya ce bayan wawason da mutanen suka yi, kayan da ya rage bai wuce na naira miliyan cassa’in ba.
Murtala Ibrahim ya kuma bayyana yadda dandazon mutanen suka farfasa motar mutumin da ke da rumbun da ya zo kai ɗauki.
Shi ma Mallam Saleh Zakiru da ke gadin rumbun ya shaida wa BBC cewa mutanen sun dira kan rumbun suna cewa “rumbun na gwamnati ne”
Ya ce wasu sun kwashi kayan ne sun fice daga Abuja zuwa wasu garuruwan.
-
News2 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion6 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
