Business
Babbar Magana: Masana sun ce nan da shekara ɗaya Naira za ta yi daraja, ta koma N1200 a Dala 1
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Katafaren Bankin Zuba Jari na Duniya, wato Goldmans Sachs, ya yi wa Najeriya kyakkyawan fatan cewa nan da watanni 12 masu zuwa, ya na sa ran darajar Naira za ta ɗaga sama zuwa Naira 1,200 a kowace Dalar Amurka 1.
Ya ce sabbin tsare-tsaren tattalin arzikin ƙasa na kurkusa da Najeriya ta bijiro da su ne za su bayar da wannan sa’idar ɗagawar darajar Naira ɗin.
Gwamnatin Tarayya Ta Fitar Da Jerin Sunayen Jihohi 14 Da Ka Iya Fuskantar Harin Ƴan Bindiga
A cikin wani bayanin da bankin ya yi a birnin New York na Amurka a ranar Alhamis, Goldman Sachs wanda a birnin na New York ne Hedikwatar sa ta ke, ya jinjina wa tunanin da Bankin CBN na Najeriya ya yi kwanan nan, inda ya ƙara danƙara wa masu ramcen kuɗaɗe kuɗin ruwa a Najeriya.
Haka kuma ya ce Naira tiriliyan 1.6 da CBN ya kaɗa wa ƙararrawa, abu ne zai zai iya ‘fidda kitse daga cikin wuta.’
Premium Times ta ruwaito cewa Naira dai ta rasa kashi 70 bisa 100 na darajar ta a cikin watanni 9 zuwa yau, inda ta tashi daga N750 duk Dala 1, har ta kai N1,680 duk Dala 1.
A yanzu dai Dala ta na Naira 1,500 da ɗoriya, a daidai lokacin da raɗaɗin tsadar rayuwa ke ci gaba da kwankwatsar talakawa da masu hali, inda farashin abinci, kayan masarufi da sauran kayayyakin amfani duk sun tashi, tun bayan tashin Dala da cire tallafin fetur.
-
News1 day ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
-
News2 days ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
