News
Tangarɗan Na’ura: Babban Bankin Ƙasar Ethiopia Ya Koma Aman Kuɗi Ba Iyaka
DAGA MARYAM BASHIR MUSA
Babban bankin kasar Ethiopia Ya sami tangarɗan na’ura wanda hakan yayi sanadiyyar fitar miliyoyin daloli, kamar yadda kafafen yaɗa labaran kasar suka bayyana.
Rahotanni sun bayyana cewa an sami fitar sama da dalar Amurka miliyan 40 daga bankin ,Kuɗaɗe ne suka yi ta fita ba iyaka.
Yadda jami’ar Hukumar Tara Haraji ta karkatar da kuɗaɗen haraji cikin makarantar kuɗi da ta gina
Shugaban bankin Abie Sano ya shaida wa taron manema labarai a ranar Litinin cewa dalibai ne suka fi kowa cire kuɗaɗe inda BBC ta ruwaito cewa an sami dogon layi a wuraren cire kuɗi.
Tuni dai Jami’o’in ƙasar suka bukaci ɗaliban da su mayar da kuɗaɗen tunda ba nasu ba ne .Haka kuma shugaban Bankin ya bayyana cewa duk wanda ya dawo da abinda ya kwasa ba za a tuhume sa ba.
Sai dai a a nata jawabin babban bankin ta shaida a shafin ta na X Cewar musabbabin faruwar wannan lamari hari ne aka kamata ta yanar gizo
