News
Ranar Tarin Fuka: Gwamnatin Kano Ta Tabbatar Da Shirye-shiryen Kawo Karshen Cutar Tarin Fuka A Jihar —Dr Labaran
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Gwamnatin jihar Kano tare da hadin gwiwar Kungiyoyi masu zaman kansu na kokari wajen ganin an kawo karshen cutar tarin fuka dake yaduwa a jihar.
Kwamishinan lafiya na jihar Dr Abubakar Labaran Yusuf ya bayyana haka a lokacin taron manema labarai kamar yadda aka saba duk shekara, ranar 22 ga watan Maris, ita ce ranar da duniya ke tunawa da kuma sabunta yaki da cutar mai hadarin gaske.
Hedikwatar Tsaro na neman su Dogo Gide, Simon Ekpa, Bello Turji da sauransu ruwa a jallo
Dr Labaran ya ce gwamnatin Kano ta kammala shirye-shirye don gudanar da gwaji da kuma bayar da maganin cutar tarin fuka kyauta a jihar Kano.
Ya yi kira ga duk mazauna jihar da su kai kansu a duba su idan suna fama da tari har na tsawon makonni biyu ko fiye, inda ya ce gwamnatin Kano ta samar da wani shiri na yi mazauna jihar gwaji da bayar da magungunan cutar.
Haka zalika ya yaba da kokarin da kungiyoyi masu bayar da tallafi ke yi wajen yaki da cutar tarin fuka da sauran cututtuka a jihar, ya ce gwamnatin kano ta dauke bangaren kiwon lafiya da Muhimmancin.
Ya ce Bisa ga alkaluma mutum 39,420 ne suka kamu da cutar inda daga ciki mutum 36,843 ke karbar magani a asibitin jihar suna samun sauki.
“Gwamnatin jihar Kano ta yi kokari wajen dakile yaduwar cutar ta hanyar ware isassun kudade domin zantar da matakan kawar da cutar a jihar.
“Gwamnati ta siyo na’urorin daukan hoto domin gwajin cutar 20 akan naira biliyan 30 a ranar 13 ga Fabrairu 2024 wanda ministan lafiya ya damka wa gwamnan jihar.
Alkaluman yaduwar tarin fuka ya nuna cewa a shekarar 2023 mutum miliyan 10.3 ne ke fama da cutar a duniya.
Zuwa yanzu Najeriya ita ce kasa ta shida a jerin kasashe 30 da suka fi fama da yaduwar cutar a duniya.
Cutar Tarin Fuka wata mummunar annoba ce da ta zama ruwan dare a duniya. Kuma ko da yake cutar na yaduwa a cikin gaggawa a nahiyar Afurka, amma ta fi addabar kasashen Asiya, wadanda ke da kashi 55 zuwa kashi 60% na illahirin masu fama da ita a duniya sai kuma kasashen Latin Amurka da na gabas ta Tsakiya da kuma kasashen gabacin Turai.
