News
Zargin Hannu A Ta’addanci: Gwamnatin Tarayya Ta Gayyaci Sheikh Gumi Domin Amsa Tambayoyi
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Gwamnatin tarayya ta ce, ta gayyaci fitaccen malamin addinin musuluncin nan na Kaduna, Ahmad Gumi domin amsa tambayoyi kan kalaman da ya yi kan ayyukan ‘yan bindiga a kasar nan.
Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris ne ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin da yake jawabi ga manema labarai a fadar gwamnati, da ke Abuja.
Harkar Noma Ce Kaɗai Za Ta Samar Da Zaman Lafiya A Najeriya — Peter Obi
Idris ya ce, Gumi bai fi karfin doka ba, don haka gwamnati ta ga ya dace ta gayyace shi domin amsa tambayoyi.
Leadership ta ruwaito cewa a cikin ‘yan shekarun da suka gabata, Sheikh Gumi ya yi fice wajen yin tsokaci kan ayyukan ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane a kasar nan.