News
Ƴan Najeriya miliyan 95 ne ke buƙatar yin rajistar katin shaidar ƙasa – HukumarNIMC
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Hukumar ƙatin ɗan ƙasa (NIMC) ta bayyana cewa har yanzu ‘yan Najeriya miliyan 95 na buƙatar yin rajistar katin shaidar ɗan kasa (NIN) domin cimma burinta na yiwa ‘yan ƙasar miliyan 200 rajista nan da shekarar 2025.
Shugaban Sadarwa na hukumar, Kayode Adegoke ne ya sanar da hakan a shafin sada zumunta na X a ƙarshen mako.
A cewar Adegoke, an bayar da sama da lambar NIN miliyan 105 ya zuwa yanzu, tare da kokarin yi wa sauran al’umma rijistar katin shaidar ƙasa a cikin shekara ɗaya ko biyu masu zuwa.
Adegoke ya bayyana mahimmancin NIN a matsayin wata alama ta musamman mai mahimmanci ga shirye-shiryen gwamnati daban-daban da aka mayar da hankali kan inganta tsaro da shugabanci da samar da ayyukan yi.
Ya kuma tabbatar da aniyar hukumar na ganin an samu yi wa dukkan ƴan Najeriya a faɗin duniya rajistar nan da shekarar 2025.
Adegoke ya lura da cewa bayan naɗin Abisoye Coker a matsayin darakta-janar na hukumar, ta gano cewa akwai buƙatar a daidaita tsarin gyare-gyare da rajista.
Ya ƙara da cewa, an samar da wani dandali na dogaro da kai, wanda zai bai wa ‘yan Najeriya na gida da waje damar yin gyare-gyaren da ya kamata, kamar canza suna da ranar haihuwa da adireshin Imel, da lambobin waya daga gidajensu ko ofisoshinsu, ta hanyar amfani da wayoyi daban-daban.
Adegoke ya jaddada cewa za a saukaka wannan dandali na dogaro da kai, inda ya buƙaci ‘yan Najeriya da su yi amfani da wannan sabuwar dabarar.
Ya yi nuni da yadda tsarin ke faruwa, inda ya ce a baya, masu son a yi musu gyara sai sun ziyarci ofisoshin NIMC domin gyara bayanansu
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
