Politics
Zan kawo cigaba mai dorewa matukar Alumma suka bani damar darewa Shugabancin Ƙaramar Hukumar Kura -Hon Salisu Kura
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Ɗan Takarar Kujerar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Kura ta Jihar Kano dake Arewacin Najeriya, Honarabul Salisu Mahmud Kura ya bayyana ƙudirinsa na mayar da ƙaramar hukumar tamkar wata ‘ ƙaramar Birnin London matuƙar al’ummar yankin suka bashi dama Jagorantarsu.
Honarabul Salisu Kura ya bayyana haka ne a yayin zantawar sa da jaridar Indaranka a safiyar yau litinin a dai-dai lokacin da ya ke bayyana aniyarsa na tsayawa takarar Shugabancin ƙaramar hukumar tasu ta Kura a ƙarƙashin Jam’iyyar NNPP, a zaɓen da ake shirin gudanarwa a watan Nuwamba me zuwa.
A cewar Honarabul Kura “Da zarar ya sami nasarar ɗarewa kan karagar mulkin ƙaramar hukumar zai bunƙasa Fannin Ilimin, samar da ayyuka da Sana’oin dogaro da kai ga Mata da Matasa, baya ga gudanar da ayyukan raya ƙasa dama maida hankali akan ingana harkar Lafiya a faɗin ƙaramar hukumar”.
A fannin Noma kuwa ya bayyana shirin da yayi na haɓɓaka harkar Noman yankin ta hanyar samar da sabbin dabaru dama ƙaro kayan noman zamani, domin bawa ƙaramar hukumar damar zama cibiyar samar da kayan noma Musamman Shinkafa a faɗin Afirka.
Adan haka ne ya nemi haɗin kai da goyon bayan al’ummar ƙaramar hukumar dama dukkan ‘yan uwa da abokan Arziƙi,ta hanyar yi masa addu’ar Allah ya tabbatar da abinda yafi zama alkhairi da wannan niyya da ya sanya a gaba.
Honarabul Salisu Kura dai yayi shura a fannin aikin jarida ta yadda ya shafe kusan shekaru 10 yana aiki da kafafen yaɗa labarai daban-daban, baya ga yadda yake gudanar da harkokin kasuwancin sa a Jihohin Arewacin Najeriya.