Connect with us

News

Kamfanin NNPCL Ya Ƙara Farashin Litar Mai Daga Naira 617 Zuwa Naira 897

Published

on

NNPCL ya ƙara farashin litar mai daga naira 617 zuwa naira 897.jpg

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Kamfanin mai na Najeriya, NNPCL ya sanar da sabon farashin litar man fetir. A wata sanarwa da kamfanin ya aike wa manema labarai, kamfanin ya ce daga yau ranar 3 ga watan Satumban 2024, kamfanin ya ƙara kuɗin litar man fetir daga naira 617 zuwa 897.

Advertisement

Tuni dai wasu gidajen maI a Najeriya suka sauya farashin litar zuwa sabon da kamfanin ya sanar a ranar ta Talata.

Zanga Zanga Ta Ɓarke Sakamakon Wahalar Man Fetur 

Wannan dai na zuwa ne kwana ɗaya bayan da kamfanin na NNPCL ya bayyana cewa yana fuskantar matsalar ƙarancin kuɗi, wani abu da ya sa ƴan Najeriya hasashen kamfanin na koƙarin sanar da sabon farashi ne.

Advertisement

Da ma dai kafin sanar da sabon farashin na ranar Talata, dogayen layukan ababan hawa sun mamaye gidajen mai a biranen Abuja da Legas.

Tun dai bayan da gwamnatin shugaba Tinubu ta sanar da janye tallafin man fetur a ranar 29 ga watan Mayun 2023, ƴan Najeriya ke fuskantar sauye-sauye a farashin man wanda kuma ke taɓa sauran sassan rayuwa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending