News
Gwamnatin Jihar Kano Ta Amin Ce Da Naira 71,000 A Matsayin Mafi Karancin Albashi

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamnatin jihar Kano da daddale matsayar naira 71,000 a matsayin mafi ƙanƙanta albashin da zata ringa biyan ma’aikatanta.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan a fadar gwamnatin jihar ranar Talata bayan ganawa da wakilan ƙungiyar ƙwadago.
Cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook Gwamnan ya ce ƙarin zai fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Nuwamban 2024.
Sanarwar ta ce hakan ya biyo bayan amincewar Kwamitin amintattu da gwamnatin Kano ta Kafa dan duba tsarin mafi Karancin albashi da gwamnatin tarayya ta bugata.
Jihar Kano ta zama ɗaya daga cikin jihohin da suka amince da biyan sama da abin da gwamnatin tarayya ta amince na N70,000 a matsayin mafi karancin albashi tun a watan Yuli.
Jihohin Legas da Rivers ne kan gaba bayan sun amince da N85,000, sai kuma Neja da ta ce za ta biya N80,000 a matsayain mafi kankantar albashi.
Akwai jihohin Najeriya da suka amince da biyan albashi mafi ƙanƙanta na N70,0