News
Kano: Fiye Da Kashi 70% Na Mata Na Zaɓar Haihuwa A Gida Duk Da Haɗarin Da Ke Tattare Da Hakan — Bincike
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Sakamakon bincike ya nuna cewa fiye da kashi 70% na mata a Jihar Kano suna son haihuwa a gida duk da haɗarin da ke tattare da hakan.
Binciken ya bayyana cewa tsadar rayuwa ba daga cikin dalilin da ke hana mata zuwa asibiti yayin haihuwa.
An bayyana wannan bayanin ne a taron kwana ɗaya kan kiwon lafiyar mata wanda Cibiyar Center for Community and Social Impact (CCSI) ta shirya a Kano ranar Alhamis.
Gwajin Ciwon Suga A Kai A Kai Ya Zama Dole Domin Cuta ce Mai Kisa a Boye
Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano, Dr. Abubakar Labaran, ya nuna damuwa game da sakamakon binciken.
Dr. Labaran ya lura cewa mata da yawa suna guje wa zuwa asibiti don kula da su kafin haihuwa da bayan haihuwa, wanda hakan yana ƙara haɗari ga lafiyar uwa da jariri.
Dr. Labaran ya bayyana kalubale da ke fuskantar yankunan karkara, inda ƙarancin samun damar zuwa asibitoci ya ƙara yawan mace-macen mata masu juna biyu a Kano da Arewacin Najeriya gaba ɗaya.
Sai dai, Dr. Labaran ya fayyace cewa alkaluman binciken sun sha bamban da na hukuma daga ma’aikatar.
“A halin yanzu muna tattara rahotonmu na shekara-shekara wanda zai bayar da sahihan bayanai,” in ji shi.
Da aka tambaye shi game da kudurin gwamnatin jiha na magance wannan matsala, Dr. Labaran ya ce, “Gwamnatin jiha ta ware sama da naira miliyan 55 don tallafa wa mata masu juna biyu da masu haihuwa a fadin jihar.”
Babbar likitar mata ta farko a Kano, Farfesa Hadiza Galadanci, ta kuma nuna damuwa game da sakamakon binciken, inda ta bayyana cewa kashi 30% kawai na mata a Kano ke zuwa asibiti don kula yayin ciki da haihuwa.
Galadanci ta nuna cewa matsalolin tattalin arziki suna daga cikin manyan Ƙalubalen da mata ke fuskanta.
Ta yi kira ga ma’aikatan kiwon lafiya da su rungumi halin jinƙai, suna duba marasa lafiya a matsayin abokan hulɗa masu muhimmanci maimakon kawai ɗaukar su a matsayin masu neman
Game da hanyoyin magance matsalar, Galadanci ta yi kira da a ɗauki matakai na zamani don rage matsaloli yayin ciki.
“Ma’aikatan lafiya suna bukatar horo kan sabbin hanyoyi, kuma tsarin kiwon lafiya ya kamata ya samar da yanayi da zai tallafa wajen amfani da su.”
-
Opinion6 days ago
Ayyuka, Bin Diddigi, Biyan Kudi, Sakamako: Dabarun Kano Da Suka Zarce Jihohi 35
-
Opinion6 days ago
Tiriliyan ₦210 na Karya: Yadda Bala Wunti Ya Warware Dukkan Rudanin da Ya Mamaye Zaman Majalisar Dattawa Kan Asusun NNPC
-
News4 days ago
Likitan El-Rufai Ya Shiga Matsala Kan Zargin Bayar Da Rahoton Jinya Na Bogi
