Connect with us

News

An Samu Karuwar Cin Zarafin Bil Adama A Daidai Lokacin Da Tattalin Arzikin Najeriya Ke Kara Tabarbarewa —Rahoto

Published

on

Dubban mutane sun fito zanga zanga a birnin Legas a ranar cikar Najeriya shekaru 64 da samun yancin kai
Wasu 'yan Najeriya yayin zanga-zanga kan tsadar rayuwa
Advertisements
Advertisements
Spread the love

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD TUKUNTAWA 

Hukumar kare hakkin dan Adam ta Najeriya ta fitar da wani rahoto da ke nuna cewa an samu karuwar yadda ake cin zarafin bil adama a daidai lokacin da tattalin arzikin kasar ke kara tabarbarewa.

Hukumar ta tattara korafe-korafe 427,606 a cikin watan Oktoba, wanda ya nuna karuwar kashi 27 cikin 100 na korafe-korafe idan aka kwatanta da watan Satumba.

Advertisement

Ana Gudanar Da Zaɓen Gwamna A Jihar Ondo

Da yake gabatar da sabon rahoton, babban mai baiwa hukumar shawara, Hilary Ogbonna, ya ce watan Oktoba ne aka fi samun rahoton yawan kashe-kashe da sace-sace a Najeriya.

Mista Ogbonna ya bayyana cewa fashewar wata tankar dakon man fetur a jihar Jigawa wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 167 na daga cikin adadin rahoton mutanen da suka mutu a watan Oktoba da aka sanya.

Sakataren zartarwa na hukumar, Tony Ojukwu, ya ce karuwar adadin da aka bayar na nuni da cewa ba za a iya kwatanta yadda ake take hakkin dan adam a sassan Najeriya.

Advertisement

 

FRI HAUSA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending