Connect with us

News

‎Jami’an Tsaro A Indiya Sun Kama Wata ‘Yar Najeriya Bisa Zargin Safarar Hodar Iblis Da Takai Gram 121 A Cikin Burodi ‎

Published

on

cover1 1766562181

‎’yan sanda sun kama wata ’yar Najeriya mai shekaru 29, Olajide Esther Iyanuoluwa, bisa zargin safarar hodar iblis da ta boye a cikin Burodi.

‎Hukumomin tsaro a birnin Bengaluru sun ce sun cafke wadda ake zargin ne yayin da take tafiya a wata bas  daga Mumbai zuwa Bengaluru, bayan samun bayanan sirri game da motsinta.

Advertisement

Jami’an EFCC Sun Bankado Wasu Kadarori Na Kimanin N212bn Da Ke Da Alaka Da Malami

‎Jaridar PUNCH ta  ruwaito a ranar Talata cewa ‘yan sanda sun ƙwace hodar iblis din da darajarta takai kimanin rufi miliyan 12 (miliyan 194,079,600 kenan a kudin Najeriya) daga hannun wadda ake zargin, lamarin da ke nuna yadda masu safarar miyagun ƙwayoyi ke ƙara amfani da abinci na yau da kullum wajen jigilar kwayoyi.

‎An bayyana sunan wadda ake zargin da Olajide Esther Iyanuoluwa. Ta je New Delhi a bara da takardar karatu (student visa), amma bincike ya nuna cewa ba ta taɓa yin rajista a kowace makaranta ba.

Advertisement

‎Maimakon haka, rahotanni sun sheda cewa tana yawan sauya matsuguni a birnin Mumbai da kewaye, ciki har da Ghatkopar (Gala Nagar), Ambawadi da Nallasopara, inda ake zargin tana aikata safarar miyagun ƙwayoyi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending