Connect with us

News

An fara yajin aiki a wasu jihohin 5 game da mafi ƙarancin albashi

Published

on

An fara yajin aiki a wasu jihohin Najeriya 15 game da mafi ƙarancin albashi

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

A Ranar Litinin ƙungiyar ƙwadagon Najeriya NLC ta shiga yajin aikin gargaɗi a jihohin ƙasar 14 da kuma birnin Abuja, biyo bayan gazawar da gwamnatocin jihohin suka yi wajen fara biyan mafi ƙarancin albashi na naira dubu 70.

Advertisement

Wasu daga cikin jihohin da yajin aikin ya shafa sun haɗa da Cross River, Enugu, Nasarawa, Katsina, da Sokoto da Zamfara sai kuma Kaduna.

Kungiyar Awareness For Human Right And Charity Foundation Ta Bayar Da Kyautar Jini Leda 150 A Kano

A zantawar Rfi Hausa da Shugaban ƙungiyar ƙwadagon Najeriyar NLC reshen jihar Kaduna, Kwamred Ayuba Magaji Suleiman, domin jin halin da ake ciki ya bayyana cewa ma’aikatan sun yi biyayya ga Uwar ƙungiyarsu ta ƙasa wajen tsunduma yajin aikin.

Advertisement

Kwamred Ayuba ya ce sun yi hakan ne domin bai wa ma’aikatansu kariya kamar yadda doka ta tanada, kuma da yawa daga cikin ma’aikata ba su fito aiki ba.

Sai dai ya ce har yanzu babu wani martani daga bangaren gwamnati game da yajin aikin da suka tsunduma, amma ƙofarsu a buɗe ta ke domin tattaunawar samun masalaha.

Advertisement

Tun a ranar 10 ga watan Nuwamban da ya gabata ne dai NLC ta bayar da wa’adin ranar 1 ga watan Disambar da muke ciki, kafin shiga yajin aikin gargaɗi a jihohin Najeriya da suka ƙi amincewa da biyan mafi ƙarancin albashin ma’aikata.

Tuni dai wasu ma’aikata a jihohin ƙasar suka fara karɓar mafi ƙarancin albashi, lamarin da ya sanya su darawa, yayin da wasu gwamnatocin jihohin suka amince da biya amma basu fara aiwatarwa ba.

Advertisement

An kai ruwa rana dai kafin a sasanta tsakanin gwamnatin Najeriya ƙarƙashin Bola Ahmed Tinubu da shugabannin Ƙungiyoyin Kwadago na NLC da TUC game da tsaida mafi ƙarancin albashin ma’aikata a ƙasar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending