News
Jami’an Hukumar NDLEA Sun Kama Wani Dilan Sayar Da Kayan Mota Da Ke Fakewa Da Sana’arsa Yana Safarar Miyagun Ƙwayoyi
Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) ta tsare wani dilan sayar da sassan motoci mai suna Levi Ubodoeze kan zargin ƙoƙarin fitar da hodar iblis da ya ɓoye a farfelar wata mota da za a kai ƙasar Angola.
A cikin wani jawabi a ranar Lahadi, mai magana da yawun hukumar NDLEA Femi Babafemi ya ce, hukumar ta shafe makonni uku tana farautarsa kafin samun nasarar kama shi.
Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Fara Ba Wa Masu Juna Biyu Kulawa Kyauta a Asibitoci 154 a Najeriya
“Bayan ƙwace hodar iblis ɗin a wani kamfanin sufurin kaya a Aspanda da ke ginin Trade Fair a Ojo a jihar Legas, a ranar 21 ga watan Fabarairu, nan take aka kira mahukunta da ke ƙasar Angola wanda ya kai ga kama wanda ke shirin karɓar hodar a can wanda hakan ne ya taimaka wajen kama wanda ya aika da hodar daga Najeriya,” in ji Babafemi.
Jami’an hukumar NDLEA suka riƙa bin diddigin Ubodoeze har gidansa da ke kan titin Ago Palace Way, Isolo a jihar Legas a ranar 6 ga watan Maris kuma nan take aka cafke shi a motarsa ƙirar KIA Sport a lokacin da yake ƙoƙarin guduwa.
A yayin caje motarsa, an samu sinadarin phenacetin mai nauyin kilogiram 75.5 da ake amfani da shi wajen sarrafa hodar. Sannan an samu na’urar auna nauyin hodar a gidansa.
Mista Ubodoeze ya amsa laifin ta’ammali da hodar iblis a yayin da yake amfani da sana’arsa ta sayar da sassan motoci a kasuwar Ladipo da ke Mushin a jihar ta Legas. Ya ce abokin harkarsa da ke Angola ne ya ba shi haske kan an kama shi wanda hakan ya sa shi kuma yake ƙoƙarin guduwa.
