News
Jami’ar Bayero Na Shirin Rufe Babbar Ƙofar Shiga Tsohuwar Harabar Ta Na Wucin Gadi
Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK) ta yanke shawarar rufe babbar kofar shiga tsohuwar jami’ar na ɗan lokaci, daga ranar 13 ga Maris, 2025, domin gudanar da ayyukan gyare-gyare.
Matakin ya zo ne a wani ƙoƙari na inganta ababen more rayuwa da kuma inganta ayyukan jami’ar.
A cewar wata sanarwa da Daraktan hulda da jama’a na jami’ar, Lamara Garba, ta fitar a ranar Lahadi, an bukaci ma’aikata, dalibai, da masu ziyara da su yi amfani da wata kofar shiga yayin da ake ci gaba da aikin.
Jami’ar ta bayyana cewa tana fuskantar duk wata matsala da rufewar zata haifar, inda ta kuma tabbatar da cewa ana ƙoƙarin kammala aikin cikin gaggawa don rage wahalhalu.
Lamara ya kara da cewa matakin yana da muhimmanci wajen samar da ingantaccen yanayi ga ɗalibai da ma’aikata, yayin da jami’ar ke ci gaba da bunƙasa.
