News
Hukumar Hisba Ta Hana Kidin Gwauro
Hukumar Hisba Ta Hana Kidin Gwauro sabida, ya sa bawa koyarwar Addinin Muslunci
Mataimakin Babban Kwamandan Hukumar Hisba, Dakta Mujahideen Abubakar, ya tabbatar da cewa hukumar ta haramta kidan gwauro sabida, yana haifar tashin hankali da fada a lokacin Ramadan.
Dakta Abubakar ya bayyana cewa Hukumar Hisba ta himmatu wajen tabbatar da bin ka’idojin addini a cikin al’umma, tare da hana duk wani abu da zai iya lalata waɗannan ka’idoji. Ya kuma yi kira ga iyaye da malamai da su taka rawar gani wajen gargadi matasa game da illolin irin wannan kiɗan.
Hukumar ta kuma yi gargadin cewa za ta ci gaba da aiwatar da doka don hana irin wannan kiɗan, tare da neman haɗin gwiwar al’umma don tabbatar da bin ka’idoji.
A cewar Dakta Abubakar, “Manufar mu ita ce kare addinin Musulunci da kuma tarbiyyar matasa bisa ga ka’idojin Islama. Duk wani abu da ya saba wa wannan manufa, za mu hana shi.”
Jaridar INDA RANKA ta ruwaito cewa Hukumar ta Hisba ta bayyana cewa za ta ci gaba da gudanar da sintiri don tabbatar da bin dokokin shari’a a cikin watan Ramadan.
