News
Yan bindiga Sun Yi Garkuwa Da Matashi A Kano
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Ƴan bindiga sun kai hari a gidan wani mai suna Alhaji Yusha’u Ma’aruf, wanda shi ne mai gudanar da asibiti mai zaman kansa a ƙauyen Zakirai, da ke ƙaramar hukumar Gabasawa a jihar Kano.
Harin ya haifar da garkuwar wani matashi mai shekara 20 da ake kira Mohammed Bello, yayin da wani ɗan gidan mai suna Abubakar ya samu rauni a hannunsa .
Jami’ar Bayero Na Shirin Rufe Babbar Ƙofar Shiga Tsohuwar Harabar Ta Na Wucin Gadi
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ƴan bindigar sun shiga gidan Alhaji Yusha’u da karfi, inda suka yi garkuwa da Mohammed Bello. Abubakar, wanda ya yi ƙoƙarin tsayar da su, ya samu rauni a hannunsa yayin da yake fafutukar kare dan uwansa.
Kakakin rundunar ƴansandan jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya bayyana cewa ƴansanda sun fara farautar ƴanbindigar domin ceto wanda aka yi garkuwa da shi .
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
