Connect with us

News

Yarinya ‘Yar Shekara 14 Ta Nutse A Kogin Chanchaga Yayin Kokarin Diban Ruwa

Published

on

drownning drown man drowns in hotel pool

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Wata yarinya ‘yar shekara 14 mai suna Elizabeth Peter daga unguwar Korokpa da ke karamar hukumar Paikoro a jihar Neja ta nutse a kogin Chanchaga a lokacin da take kokarin diban ruwa. Lamarin ya faru ne a ranar Asabar, inda Elizabeth ta je kogin tare da ’yan’uwanta domin diban ruwa, amma ta yi hatsari yayin da ta fada cikin rami mai zurfi a cikin kogin.

Advertisement

Yan bindiga Sun Yi Garkuwa Da Matashi A Kano

Elizabeth, dalibar SSS1 na Saint Andrew Academy, Tunga Minna, an ce tana daya daga cikin wadanda kogin ya rutsa da su. Mazauna yankin sun bayyana cewa ana samun mace-mace a duk shekara saboda zurfafan ramuka da ke cikin kogin, wanda ke haifar da hatsarin ga mutane da yawa.

Kawarta, Misis Abigail Idoko, ta ce ga Elizabeth, shi ne karon farko da ta je kogin ranar Asabar bayan ta kasa samun masu sayar da ruwa da za su saya. Ta kuma bayyana cewa an dauki kimanin sa’o’i biyu kafin a ceto Elizabeth daga daya daga cikin ramukan da ke da zurfi.

Advertisement

A lokacin da wakilin DAILY TRUST ya ziyarci ‘yan uwan wadanda suka rasu a Korokpa, mahaifiyarta ta cika da mamaki, yayin da aka ce mahaifinta, Mista Peter, wani jami’in soji yana jihar Zamfara yana bakin aiki.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending