Connect with us

News

Iyayen Yara sun fara kokawa akan Karin kudin da Jami’ar Bayero da ke Kano ta yi.

Published

on

Buk

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

 

lyaye sun fara kokawa da karin kudi ga sabbin dalibai masu karatun digiri na farko da Jami’ar Bayero da ke Kano ta yi.

Advertisement

A wani sako da Jami’ar ta wallafa a shafinta na Facebook, ta bayyana karin kudin daya girgiza hantar iyayen yara.

Wannan karin na zuwa ne makonni bayan gwamnatin Nijeriya ta sanar da fito da tsarin bai wa dalibai bashin kudin karatu mara kudin ruwa, wanda tun a lokacin aka soma hasashen cewa za a yi karin kudin makaranta a fadin kasar.

Advertisement

A cikin sanarwar da ta fitar mai dauke da sa hannun mukaddashiyar magatakardanta, Amina Umar Abdullahi, bayan kammala taron Majalisar Gudarwarta karo na 405 wanda aka gudanar a ranar Litinin, 19 ga watan Yuni, Jami’ar ta Bayero ta bayyana cewa karin zai soma aiki ne a zangon karatu na 2022/2023.

Sarkin Kano ya sake nada Hakimai takwas

Daliban tsangayoyin koyar da Fasaha da Addinin Musulunci da Shari’a da Ilimin Zamantakewa da Kimiyyar Gudanarwa za su rinka biyan naira 95,000 a matsayin kudin makaranta a duk shekara sa’annan sabbin dalibai a tsanagayoyin za su biya naira 105,000, kamar yanda jaridar Indaranka ta ruwaito.

Advertisement

Daliban tsangayoyin koyar da Aikin Banki da Hada- Hadar Kudi da Lissafin Kudi za su koma biyan Naira 97,000, inda sabbin dalibai kuma su biya naira 107,000.

Dalibai daga tsangayoyin koyar da Ilimin Kwamfuta da Sadarwa da Kasa da Muhalli za su rinka biyan Naira 100,000, sai kuma sabbin dalibai su biya 110,000. Dalibai daga tsangayar koyar da Ilimin Sinadaren Kasa da kuma tsangayar koyar da Tsara Taswirar Birane za su koma biyan naira 105,000, sa’annan sabbin dalibai su biya Naira 115,000.

Advertisement

lyaye da daliban da suka yi tsokaci a kasan wannan sakon da aka wallafa, sun nuna damuwa matuka da wannan karin. Suka ce wannan take-take ne ‘ya’yan talakawa damar yin karatu a jam’o’in nan.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending