Connect with us

News

Sarkin Kano ya sake nada Hakimai takwas

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero CFR, JP CNOL, ya nada hakimai takwas domin inganta ci gaban masarautar jahar kano.

Hakan na kunshe ta cikin wata Sanarwar da Babban Sakataren Yada Labarai na Masarautar Kano Abubakar Balarabe Kofar Naisa yaraba manema labarai a yau litinin

Advertisement

Alhaji Aminu Ado Bayero, ya ce an yi musu rawani ne saboda gudunmawar da suke bayarwa wajen ci gaban jihar kano.

Za’a Samu Gajimare Da hadari Daga Yau Zuwa Ranar Laraba A Fadin Kasar Nan – NiMet

Sarkin ya umarce su da su yi amfani da dimbin gogewar da suka samu wajen ciyar da masarautar gaba, musamman ta fuskar addini, tattalin arziki da Kuma harkar lafiya da ilimi.

Advertisement

Ya kuma gargade su da su guji duk wani abu da ya sabawa ka’ida da al’adun mutanen jihar kano.

Wadanda aka yiwa nadin sun Hadar da  Alhaji Balarabe Adamu yakasai, Wanda akafi  sani da Bala wakili a matsayin falakin Kano, Alhaji Sulaiman Isyaku Umar Tofa a matsayin Dan Adalan Kano, Ambassador Ahmed Ibrahim Yakasai a matsayin kachallan kano.

Advertisement

Sauran sun hadara da Alhaji Usman Ado Bayero, SK Dan iyan kano, Alhaji Salim Abubakar Bayero Uban Gari, Alhaji Yusif Sambo Jakadan kano, Alhaji Muhd ​​Sani Ungogo a matsayin Kuyan Bana, da Ambassador Muhammad Yahaya, Uban Dawaki.

A nasu jawabansu na daban sabbin hakimai sun godewa Allah madaukakin sarki da sarkin kano bisa nadin nadin na ceto Al’ummar jihar da ma kasa baki daya sun halarci bikin nada rawani wanda aka gudanar a fadar sarkin Kofar Kudu.

Advertisement

 

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending