Connect with us

News

Ƙungiyar ASUU ba su taɓa yajin aiki domin talaka ba – Bulama Bukarti

Published

on

Bulama bukarti

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

Fitaccen lauyan kare hakkin bil’adama Dr. Audu Bulama Bukarti, ya ƙalubalanci ƙungiyar malaman jami’o’in Najeriya ASUU kan cewa ba su taɓa shiga yajin aiki domin talaka ba.

Dr. Bukarti ya bayyana haka ne a cikin wani rubutu da ya yi a shafinsa na Facebook a safiyar yau Litinin kamar yadda Labarai24 ta samu kwafi.

Advertisement

Za’a Samu Gajimare Da Tsawa Daga Yau Zuwa Ranar Laraba A Fadin Kasar Nan – NiMet

Ga rubutun kamar haka:

Yanzu dai an yi walkiya kowa ya ga ASUU a fili. ASUU ba taɓa yajin aiki don dan talaka ba. Lokacin da ‘yan kanzagin kungiyar suka kama karyar cewa suna yajin aiki ne don Mallam Talaka, mun kalubalance su cewa su kawo mana misalin lokaci daya tal da ASUU ta yi yajin aiki don an kara kudin makaranta, amma suka kasa. Saboda haka, mu ka ce musu a baya ASUU ba ta ta6a yajin aiki domin an kara kudin makaranta ba kuma a gaba ma ba za yi ba. Don haka ba abin mamaki ba ne don ASUU ta yi tsit yanzu. Hasalima matsawa gwamnati da ASUU ta yi daya ne daga dalilan da suka sa ake ta wannan kare-karen.

Advertisement

Karin kudin makaranta zai yi matuqar cutar da ‘ya’yan talakawa. Amma duk da haka, gwara kari da a rufe makarantun kwata-kwata kamar yadda ASUU ta saba yi. Ai da babu gwara ba dadi. Da babu gwara da tsada. Game da wadanda ba za su iya biya ba kuwa, ina kira ga jami’o’i da su duba yiwuwar sassauto da kudin makaranta. Haka kuma, ya kamata jami’o’i su duba hanyoyin tallafawa dalibai mara sa karfi. Ina kira ga Gwamnatin Tarayya da ta inganta tsarin “Student Loan” ta yadda duka mai bukata zai samu. Sannan ina kira ga masu hannu da shuni da su tallafawa dalibai masu karamin karfi.

In shaa Allah, idan lokacin registration din BUK da FUGA ya yi zan tallafawa wani adadin dalibai da wani bangaren na kudin registration. Ina kira ga masu dama-dama irina cewa suma su ma su yi haka. Ba sai ka zama biloniya za ka iya taimakawa ba. Muna rokon Allah da ya tallafi ‘yan’uwanmu, Ya ba su hanyar daukan dawainiyar karatunsu ko na ‘ya ‘yanzu. Allah Ya yi mana sutura baki daya.

Advertisement

Wasu bayanai sun nuna cewa kungiyar ta ASUU ta daka yajin aiki fiye da sau 15 tun bayan komawar Najeriya mulkin dimokuradiyya a 1999, lamarin da kan jefa harkokin karatu cikin mawuyacin hali.

Haka kuma yajin aikin malamai a Najeriya ya fi yin tasiri a kan dalibai wadanda ke tsintar kansu cikin damuwa, dalilin da ya sa wasu ke ganin ya kamata kungiyar ta sauya salon tunkarar rikicinta da gwamnatin kasar ba sai lallai ta hanyar yajin aiki ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending