News
Za’a Samu Gajimare Da hadari Daga Yau Zuwa Ranar Laraba A Fadin Kasar Nan – NiMet
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Hukumar kula da yanayi ta najeriya, NiMet, ta yi hasashen cewa za’asamu gajimare da tsawa farawa daga yau zuwa Ranar Laraba a fadin kasar nan.
Sakamakon yanayi nahukumat ta NiMet da aka fitar jiya a Abuja ya yi hasashen cewa za’a samu hadari a ranar Litinin da tazarar lillimi a yankin Arewa tare da yiwuwar tsawa da safe a sassan jahar Taraba da Kebbi.
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya rantsar da sabbin Kwamishinonin Jihar su 19
A cewar hukumar, ana iya samun tsawa a sassan jihohin Borno, Jigawa, Adamawa, Bauchi, Gombe, Kaduna, Taraba, Kano, Katsina, Zamfara da kuma Kebbi.
Hukumar ta kuma yi hasashen tsawa da ruwan sama na tsaka-tsaki a yawancin sassan yankin a nan gaba musamman da rana.
Haka Kuma Hukumar ta NiMet,ta Kara da cewa ana sa ran samun yanayin gajimare a yankin arewa da safiyar gobe Talata.
