Connect with us

News

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta buƙaci masu shirin zanga-zanga su sauya ranar yin gangamin

Published

on

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta buƙaci matasan da ake shirin gudanar da wata zanga-zanga da aka yi wa take da “Take it Back Movement” da su janye wannan ƙuduri.

Rundunar a cikin wata sanarwa da ta fitar ta shafinta na Facebook, ta ce, ta karanta a wasu kafofin yaɗa labarai cewa matasan sun ayyana ranar 7 ga watan Afirilu domin gudanar da zanga-zangar wanda ya ci karo da ranar ‘yan sanda ta Najeriya.

Advertisement

 

A cewar jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi, matasan sun shirya yin zanga-zangar ne a faɗin jihohin Najeriya, musamman a babban birnin tarayya a Abuja.

Advertisement

Barawo Ya Hadiye Dan Kunnen Zinare Na Naira Biliyan 1

“Duk da cewa ba muna ƙalubalantar ‘yancin da suke da ita ba ne na ƙungiyanci da gudanar da zanga-zangar lumana wadda kundin tsarin mukin Najeriya ya ba su dama, sai dai mun damu ne da irin manufar da ke tattare da shirya zanga-zangar a ranar da muke shirin yin bikin ranar ‘yan sanda ta ƙasa.”

Sanarwar ta ce akwai fargaba kasancewar ana sa ran halartar manyan baki daga ciki da wajen ƙasar nan, ciki har da manyan sufetocin ‘yan sanda na ƙasashe daban-daban da manyan jami’an diflomasiyya.

Advertisement

“Babban abin damuwarmu shi ne yadda aka ayyana ranar wannan biki domin gudanar da zanga-zangar wanda ka iya zama wani yunƙuri na yi wa hukumar zagon ƙasa ko ɓata mata suna da ƙasar nan bakiɗaya,” a cewar sanarwar.

Don haka, rundunar ke shawartar masu shirya zanga-zangar da su dakatar da shirinsu saboda rashin dacewar lokacin da suka saka tana mai ba wa masu shirya gangamin shawarar bin hanya ta tattaunawa da hukumomin gwamnati da abin ya shafa domin matsa musu lamba wajen biya musu buƙatunsu.

Advertisement

Sanarwar ta bayyana cewa rundunar ‘yan sandan Najeriya a ƙarƙashin jagorancin Kayode Egbetokun, ta shirya wajen gudanar da ayyukanta bisa tanadin doka da mutunta ‘yancin da ‘yan ƙasa ke da shi na gudanar da zanga-zanga.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending