News
Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane 40, Sun Kona Gidaje 383 A Filato
A kalla mutane 40 ne suka rasa rayukansu, yayin da sama da mutane 1,000 suka rasa matsugunansu sakamakon harin da wasu ‘yan bindiga suka kai a makon jiya a kauyen Hurti da ke yankin Manguna a karamar hukumar Bokkos, jihar Filato.
Hakazalika, gidaje 383 ne aka kona kurmus, tare da lalata kayayyakin abinci da wasu kayayyakin amfanin yau da kullum.
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta buƙaci masu shirin zanga-zanga su sauya ranar yin gangamin
Hakkin wannan bayanin ya fito daga bakin Dagacin kauyen Hurti, Mista Maren Aradong, yayin da Sakataran Gwamnatin Jiha (SSG), Mista Samuel Jatau, ya jagoranci tawagar jami’an gwamnati domin duba barnar da aka yi.
Kamfanin Dallancin Labarai Kasa (NAN) ya tabbatar da cewa ‘yan bindigar sun kai farmaki ne a ranar 2 ga Afrilu a kauyukan Hurti, Josho, Daffo da wasu kauyuka a yankin.
Gwamnan jihar, Kaleb Mutfwang, ya bayyana cewa hare-haren ba rikicin manoma da makiyaya ba ne,
Gwamnati ta tabbatar da kudirinta na kara tura jami’an tsaro a yankunan da lamarin ya shafa da kuma tallafawa wadanda suka rasa matsugunnai da ‘yan uwansu.
-
News7 days ago
An Tsare Kwamandan NSCDC Da Wasu Jami’an hukumar Da A Ke Zargi Da Sakaci A Mutuwar Masu Hakar Ma’adanai 37 A Neja
-
News6 days ago
Dakarun Soji Sun Ceto Ɗalibai 6 Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Katsina
-
News5 days ago
NLC Za Ta Fara Fafutukar Neman Sabon Ƙarin Mafi Ƙarancin Gabanin 2027 — Ajaero
