News
Yadda Gwamnoni 20 Suka Ƙi Biyan Mafi Ƙarancin Albashin Dubu 70,000
Shugaban ƙungiyar ma’aikatan ƙananan hukumomi ta ƙasa (ALGON), Alhaji Haruna Ƙanƙara, ya bayyana cewa har yanzu jihohi 20 a Najeriya ba su fara biyan sabon tsarin mafi ƙarancin albashi na naira 70,000 ba, duk da cewa shugaban ƙasa ya amince da dokar biyan albashin tun ranar 29 ga Yuli, 2024.
Ƙanƙara ya bayyana hakan ne yayin wata zantawa da ya yi da Jaridar Punch, inda ya nuna damuwa kan yadda aka bar ma’aikatan ƙananan hukumomi da malamai cikin rashin kulawa, musamman a wasu daga cikin jihohin da suka haɗa da Yobe, Gombe, Zamfara, Kaduna, Imo, Ebonyi, Cross River, Abuja da Borno.
Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane 40, Sun Kona Gidaje 383 A Filato
Ya bayyana cewa wasu daga cikin jihohin sun fara biyan sabon albashin ga ma’aikatan jiha, amma suka watsar da malamai da ma’aikatan ƙananan hukumomi. Wasu kuma sun yi alkawarin biyan sabon albashin amma suka kasa aiwatar da shi.
Kazalika, Ƙanƙara ya yi kira da a gaggauta shawo kan wannan matsala, yana mai jaddada bukatar samar da adalci ga ma’aikatan da ke ƙasa.
A wani bangare na batun, shugaban ya bayyana cewa babban bankin ƙasa har yanzu bai fitar da tsarin da zai bai wa ƙananan hukumomi ‘yancin bude asusun ajiyar banki ba, wanda hakan ke hana su samun ‘yancin gudanar da harkokinsu cikin ‘yanci da gaskiya.
Duk da haka, shugaban NULGE na jihar Kwara, Seun Oyinlade, ya tabbatar da cewa gwamnatin jiharsa ta fara biyan sabon albashin tun watan Oktoba 2024, inda ya bayyana hakan a matsayin mataki na gaba wajen inganta rayuwar ma’aikata.
