Connect with us

News

Ba Na Taƙaddama Da Yara — Amaechi Ya Mayar Da Martani Kan Wike

Published

on

Wike Ya Dakatar Da Sakatare Janar Na Hukumar FCDA Har Sai Baba Ta Gani

Tsohon Ministan Sufuri kuma tsohon Gwamnan Jihar Ribas, Rotimi Chibuike Amaechi, ya ce ba ya ganin dacewar yin cacar baki da wanda ya raina a siyasa, yana mai cewa “ba na taƙaddama da yara.”

Amaechi ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Arise, yayin da yake mayar da martani kan wata magana da Ministan Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya yi masa a makon jiya.

Falaloli 12 Da Ya Kamata Ku Sani Kan Ranar Arafa

Tun da fari, Amaechi ya ce a wajen bikin cikarsa shekaru 60 da haihuwa cewa, “dukkanku muna jin yunwa,” kalma wadda Wike ya maida martani da cewa, “yunwar Amaechi ba ta abinci ba ce, yunwar mulki ce.”

Sai dai Amaechi, a martaninsa, ya ce bai ga dalilin maida martani da gardama da mutumin da ya raina a siyasa ba, domin kuwa shi ne ya ba Wike dama a lokacin da yake gwamnan jihar Ribas.

Ya ce: “Ni ne na naɗa Wike a matsayin shugaban ma’aikata lokacin da nake gwamna. Na fi so in sanya ido a kansa fiye da in ba shi kujerar kwamishinan kuɗi.”

Amaechi ya ce komawar sa gwamna a Jihar Ribas ya kasance ne ta ƙaddarar Allah, da taimakon tsohon gwamna Peter Odili, da kuma goyon bayan Ma’aikatar Shari’a da al’ummar jihar.

Advertisement

Ya ƙara da cewa: “Ku tambaye shi (Wike) ta yaya ya mayar da ni gwamna. Ina faɗar haka ne domin ba na son yin taƙaddama da yara.”

Amaechi ya ci gaba da zargin Wike da cewa yana da halin ɗagawa kansa matsayi fiye da yadda ya kamata.

“Shi ya mayar da kansa shugaban ma’aikata, ya mayar da kansa gwamna, ya naɗa kansa minista, har da cewa shi ne shugaban ƙaramar hukuma,” in ji shi.

Wannan sabuwar fafatawa ta kara bayyana irin yadda alakar Amaechi da Wike ke ci gaba da yin tsami, duk da tarihin da ke tsakaninsu a tafiyar siyasa tun daga lokacin da Amaechi ke rike da madafun iko a jihar Ribas.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending