News
Gwamnatin Tarayya Ta Sake Jaddada Matsayarta Ta Ƙin Ƙarbar Baƙi Da Amurka Ke Kora
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sake jaddada matsayar ta ta kin karɓar bakin da Amurka ke kora daga kasarta, inda ta nesanta kanta da matakin da kasashe irinsu Rwanda da Eswatini da Sudan ta Kudu suka ɗauka na baya-bayan nan da suka amince da karɓar ‘ƴan ƙasashen waje da aka kora daga Amurka.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Najeriya, Kimiebi Ebienfa, wanda ya tabbatar wa jaridar PUNCH matsayar gwamnati, ya jaddada cewa Najeriya ta tsaya tsayin daka a kan matsayinta, saboda matsalolinta na cikin gida kama daga tsaro da tattalin arziki.
A watan Yulin da ya gabata ministan Harkokin Wajen Najeriya, Yusuf Tuggar, ya bayyana cewa gwamnatin Shugaba Donald Trump na ƙara matsawa ƙasashen Afirka lamba domin su amince da karɓar mutanen da ta kora ciki harda waɗanda aka samu da aikata manya laifuka.
Amb. Tugar ya ce Amurka na ƙara matsa lamba kan ƙasashen Afirka da su amince da karɓar wasu ƴan ƙasar Venezuela masu aikata laifuka da ke tsare a gidajen yari.
Ya kuma bayyana matakin a matsayin wanda ba za a amince da shi ba, yana mai cewa irin wannan manufar za ta yi wa ƙasashe irin su Najeriya nauyi bisa la’akari da ƙalubale na cikin gida da ake fuskanta.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
