News
Matsalar Ƙwacen Waya Da Faɗace-Faɗacen Daba Na Ci Gaba Da Ci Wa Kanawa Tuwo A Ƙwarya
Matsalar ƙwacen waya da rikice-rikicen ’yan daba na ƙara tsananta a Jihar Kano, inda al’amuran suka kai ga salwantar rayukan mutane a makonnin baya-bayan nan.
A ƙarshen makon da ya gabata, an yi wa Sadiq Gentle, babban mai taimaka wa Gwamnan Kano a Hukumar Tarihi da Al’adu, kisan gilla bayan wasu da ake zargin ’yan daba ne sun kai masa hari a gidansa. Maharan sun caccaka masa makami a wurare da dama, lamarin da ya sa aka yi masa tiyata, kafin daga bisani ya rasu a ranar Alhamis.
Gwamnatin Tarayya Ta Sake Jaddada Matsayarta Ta Ƙin Ƙarbar Baƙi Da Amurka Ke Kora
A cikin wannan watan nan ma, wani ɗalibin Jami’ar Bayero Kano, Umar Abdullahi Hafizi, ya rasa ransa sakamakon harin masu ƙwacen waya a cikin birnin.
Rahotanni sun nuna cewa matsalar ta yi kamari sosai, inda kusan babu rana a Kano da ba a samu labarin faɗan ’yan daba ko kuma ƙwacen waya a wasu sassan jihar ba.
Wannan na jefa al’umma cikin fargaba, inda ma wasu unguwanni aka daina ziyarta musamman idan dare ya yi.
Masana harkokin tsaro da zamantakewa na danganta yawaitar wannan matsala da talauci, rashin aikin yi, ƙarancin tsaro da kuma gazawar hukunta masu aikata laifi.
Sai dai lamarin ba Kano kadai ya shafa ba, domin a watan Yuni da ya gabata wani soja ya rasu a Jihar Kaduna bayan wani mai ƙwacen waya ya caka masa wuƙa a ƙirji.
Masana da hukumomin tsaro sun yi kira ga gwamnatin jihar da ta ƙara tsananta matakan tsaro, tare da tabbatar da cewa duk wanda aka kama da hannu a irin wannan laifi an gurfanar da shi gaban kuliya cikin gaggawa.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
