News
Dalilin Janye Takardar Kammala Hidimar Ƙasa Ta Rita Uguamaye —NYSC
Hukumar kula da masu yi wa ƙasa hidima ta ƙasa (NYSC) ta karyata zargin cewa ta janye takardar Dalilin Janye Takardar Kammala Hidimar Ƙasa Ta Rita Uguamaye saboda maganganunta na suka kan Shugaba Bola Ahmed Tinubu ko gwamnatin tarayya.
A wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Lahadi, NYSC ta bayyana cewa matakin ya samo asali ne daga karya ƙa’ida, inda Rita ta gaza halartar tantancewar zanen yatsa na watan Afrilu 2025. Wannan, a cewar hukumar, ya saba wa dokokin ciki, abin da ya sa aka tsawaita hidimarta da wata biyu.
“Uguamaye tana cikin jerin ‘yan hidima 131 da aka tsawaita shekarar hidimarsu saboda dalilai daban-daban. Wannan hukunci ba na musamman bane gareta, kuma babu wata alaƙa da siyasa,” in ji hukumar.
Tun da fari, Rita ta yi fice a shafukan sada zumunta bayan ta yi suka kan jinkirin biyan sabon kuɗin alawus ga masu yi wa ƙasa hidima, daga N33,000 zuwa N77,000, wanda gwamnati ta amince da shi amma ta jinkirta aiwatarwa. A cikin wani bidiyo, ta zargi gwamnati da jefa ‘yan hidima cikin ƙuncin rayuwa saboda wannan jinkiri.
