News
An Nada Akwaden Stephen Thomas a Matsayin Shugaban ICAN na 7 Reshen Lafiya
DAGA JOHN WADA, KEFFI
Ƙungiyar ƙwararrun masu lissafin kuɗi ta Najeriya, The Institute of Chartered Accountants of Nigeria (ICAN), reshen Lafiya, jihar Nasarawa, ta gudanar da babban taron nadin sabon shugabanta, Mista Akwaden Stephen Thomas, FCA, a matsayin shugaban ƙungiyar na 7, tare da ƙaddamar da sauran sabbin jagororin kwamitin gudanarwar ƙungiyar na shekarar 2025 zuwa 2026.
Taron, wanda aka gudanar a babban ɗakin taron jami’ar jihar Nasarawa da ake kira S.B. Mohammed Auditorium, ya samu halartar manyan baƙi daga sassa daban-daban, ciki har da tsohon mataimakin shugaban jami’ar, Farfesa Suleiman Bala Mohammed, da Farfesa G.A. Amuga, da sauran jami’ai da mambobin ƙungiyar.
Dalilin Janye Takardar Kammala Hidimar Ƙasa Ta Rita Uguamaye —NYSC
A jawabinta a yayin taron, Shugabar Jami’ar Jihar Nasarawa, Farfesa Sa’adatu Hassan Liman, wacce Farfesa Maikano Ari ya wakilta, ta gode wa ICAN bisa zaben Akwaden a matsayin sabon shugaba. Ta yaba da kwarewarsa a fannin lissafin kuɗi tare da tabbatar da cikakken goyon bayan jami’ar ga shugabancin nasa.
Ta ce, “Stephen Thomas Akwaden mutum ne mai gaskiya, kyakkyawan hali da mutunci. A madadin Jami’ar NSUK, za mu ci gaba da nuna masa goyon bayanmu tare da tabbatar da haɗin gwiwa mai amfani don ci gaban ƙungiyar, jami’ar, da al’umma baki ɗaya. Ina kira ga mambobin ƙungiyar su ba shi cikakken haɗin kai domin samun nasarori.”
A nasa jawabin bayan ƙaddamar da shi, Mista Akwaden ya bayyana nadin nasa a matsayin lokaci na alfahari da kuma alƙawari na hidima ga ƙungiyar. Ya ce, shugabancinsa zai mayar da hankali kan inganta sana’o’i, faɗaɗa tasiri da kuma ci gaba da gina ƙungiyar bisa ginshiƙai guda biyar — ƙara yawan ɗalibai da matasa, shirye-shiryen horo na ci gaba (CPD), ayyukan al’umma, haɗin gwiwa na ilimi, da ƙarfafa tsarin mulki da gado.
Ya kuma sanar da cewa zai ɗauki nauyin ɗalibai 50 da suka kammala digiri a Jami’ar Jihar Nasarawa domin yin jarrabawar ICAN.
Daga ƙarshe, tsohon mataimakin shugaban jami’ar, Farfesa Suleiman Bala Mohammed, da Farfesa G.A. Amuga, sun yaba wa Akwaden bisa gudummawar da ya bayar wajen ci gaban jami’ar, tare da taya shi murna bisasabon mukamin.
