News
Gobarar Tankokin Mai Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutane da Dama a Zariya
Ana fargabar cewa mutane da dama sun mutu a safiyar Litinin sakamakon gobarar da ta tashi bayan tankokin mai biyu sun yi bindiga a Ɗan Magaji, ƙaramar hukumar Zariya, Jihar Kaduna.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 8:30 na safe, a kusa da Makarantar Rochas Foundation, kan titin Kaduna–Kano bypass daga Kwangila zuwa Ɗan Magaji.
An Nada Akwaden Stephen Thomas a Matsayin Shugaban ICAN na 7 Reshen Lafiya
Shaidu sun ce hatsarin ya haɗa manyan motocin dakon mai guda biyu da kuma motoci biyu ƙirar Golf masu ɗauke da fasinjoji. Bindigar tankokin mai ɗin ta haddasa wuta mai ƙarfi tare da hayaƙi mai kauri da ya rufe hanyar.
Jami’an ceto da tsaro sun rufe hanyar gaba ɗaya, tare da gargaɗin direbobi da su guji wucewa ta yankin, yayin da ake ci gaba da aikin ceto da kwashe gawarwaki.
Har zuwa lokacin da ake samun wannan rahoto, ba a tabbatar da adadin mutanen da suka mutu ko suka jikkata ba, sai dai an ce aikin ceto na ci gaba.
