Connect with us

News

Gwamna Ya Sauke Kwamishinoni 19

Published

on

Gwamnonin Najeriya

Gwamnan jihar Ekiti, Mista Biodun Oyebanji ya sanar da sauye-sauye a majalisar zartarwa ta jihar nan take biyo bayan sallamar kwamishinoninsa 19.

‎Sallamar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakatariyar gwamnatin jihar, Farfesa Habibat Adubiaro ta sanya wa hannu, kuma ta mika wa manema labarai a yammacin jiya Lahadi.

Gobarar Tankokin Mai Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutane da Dama a Zariya

‎Kwamishinonin da abin ya shafa da masu ba su shawara na musamman a cewar sanarwar, an umurce su da su mika ragamar ofishinsu ga babban sakatare ko babban ma’aikacin gwamnati a hukumominsu.

‎Gwamna Oyebanji ya godewa ‘yan majalisar zartarwar jihar da abin ya shafa tare da yi musu fatan samun nasara a ayyukansu na gaba.

‎Sai dai, umarnin bai shafi babban Lauyan jihar da kwamishinan shari’a ba.

‎Har ila yau, daga cikin wadanda sallamar ba ta shafa ba, akwai Kwamishinonin Lafiya da Ayyukan Jama’a, Noma da Tattalin Abinci da Ayyuka.

Advertisement

‎Bugu da kari, kwamishinan ciniki, saka hannun jari, masana’antu da kungiyoyin hadin gwiwa; Mai ba da shawara na musamman kan Ilimin masu bukata ta Musamman; da mai ba da shawara na musamman kan tsare-tsaren kasa, duk suna nan kan mukamansu.

‎Haka kuma, duk Daraktocin da ke cikin majalisar zartarwa ta Jihar, za su ci gaba da rike mukamansu.

 

 

 

LEADSHIP HAUSA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending