News
Mutumin Da Ake Zargi Da Ajalin Jami’in Civil Defence Ya Rasu A Hannun Hukumar A Jigawa
Hukumar Tsaro ta Civil Defence (NSCDC) a Jihar Jigawa ta ce wani da ake zargi da kashe jami’inta, Bashir Adamu Jibrin, ya rasu a hannun jami’an tsaro yayin da ake kaishe zuwa hedikwatar hukumar a Dutse.
Wani jawabi da mai magana da yawun hukumar, Muhammad Badarudeen, ya fitar a ranar Alhamis ya ce wanda ake zargin, Salisu Muhd, mai shekara 45, an kama shi ne a ranar 7 ga Agusta, 2025, a gidansa da ke garin Shuwarin, Karamar Hukumar Kiyawa.
A cewar NSCDC, rahotanni sun nuna cewa a lokacin wani samame a kasuwar Shuwarin, Salisu ya bugi jami’in da dutse a kai, lamarin da ya yi sanadin mutuwar jami’in.
Sai dai hukumar ta ce yayin da ake tafi da wanda ake zargin zuwa hedikwata a Dutse, ya yi ƙoƙarin tserewa ta hanyar tsalle daga cikin motar da ke tafiya da gudu, abin da ya janyo masa mummunan rauni. An garzaya da shi asibitin gwamnati a Dutse, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.
Rahoton likita daga asibitin Sambo Hospital Limited da ke Dutse, wanda dangin mamacin suka nema, ya nuna cewa Salisu ya rasu ne sakamakon raunin da ya samu bayan tsalle daga motar.
Sai dai har yanzu akwai tambayoyin da ba a amsa ba, musamman kan yadda tsallensa daga motar ya yi sanadin mutuwa nan take, da kuma matakan tsaro da aka ɗauka a yayin jigilar wanda ake zargi.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
