News
BBC Hausa Ta Ƙi Karɓar Ajiye Aikin Shugabanta Aliyu Tanko, Ta Dakatar da Shi Tsawon Watanni Uku
BBC Hausa ta ƙi karɓar takardar ajiye aikin da shugaban sashin, Malam Aliyu Tanko, ya gabatar a yau Alhamis, inda hukumar ta sanar da dakatar da shi na tsawon watanni uku domin gudanar da bincike.
Wannan mataki ya biyo bayan wata hira da aka yi da tsohuwar shugabar sashin sadarwa ta BBC Hausa, Hajiya Halima, wadda ke aiki yanzu a TRT Hausa. A hirar, ta yi zargin cewa wani babban jami’in kafar ya yi mata barazana da gallaza mata a lokacin da take aiki a BBC, abin da ya tilasta mata yin murabus daga aikin. Duk da cewa ba ta ambaci sunan jami’in ba, zargin ya tayar da ƙura a kafar.
Gwamnatin Tarayya Ta Musanta Cimma Wata Yarjejeniya Da ASUU – Ministan Ilimi
Rahotanni sun tabbatar da cewa babban ofishin BBC da ke Landan ya turo tawagar bincike zuwa Abuja ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban kafar, Jonathan Moro, domin binciko gaskiyar lamarin.
A cewar jaridar Solacebase, BBC ta ƙi karɓar ajiye aikin Tanko ne saboda ba a bin ƙa’idodin ajiye aiki yayin bincike. Mahukunta sun bayyana cewa, ba zai iya barin aiki ba har sai an kammala bincike, kuma idan ya nace sai ya yi murabus, to ya biya BBC albashin watanni biyu.
-
News1 day ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News22 hours ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News2 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
