News
Yan Bindiga Sun Hallaka Jami’in Sa-kai, Sun Sace Matan Fitaccen Dan Kasuwa A Kano
Wasu ƴan bindiga sun kai hari a garin Kafin Maiyaki da ke ƙaramar hukumar Kiru, jihar Kano, inda suka kashe wani jami’in sa-kai sannan suka yi garkuwa da matan wani fitaccen ɗan kasuwa a yankin.
Shaidun gani da ido sun ce maharan sun kai samame gidan Alhaji Ibrahim Ahmad Rufai, shugaban ƙungiyar ƴan kasuwar Kafin Maiyaki, inda suka yi awon gaba da matansa zuwa wurin da ba a sani ba.
BBC Hausa Ta Ƙi Karɓar Ajiye Aikin Shugabanta Aliyu Tanko, Ta Dakatar da Shi Tsawon Watanni Uku
A yayin harin, wani ɗan sa-kai da ya yi ƙoƙarin kare al’umma daga farmakin maharan ya rasa ransa.
Wani masani kan tsaro a yankin, Bakatsine, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Alhamis ta hanyar wallafa sanarwa a shafinsa na X.
Har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa kanharin ba.
-
News21 hours ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
-
News1 day ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
