Connect with us

News

Farashin Kayan Abinci Ya Sauka A Kasuwanni, Amma Masu Dafa Abinci Sun Ki Rage Kuɗi —Rahoto

Published

on

IMG 20250905 WA0012

Rahotanni daga hukumomin kididdiga da binciken kasuwanni sun nuna cewa farashin kayan abinci ya ragu a Najeriya, musamman masara, shinkafa, doya, wake da garin rogo.

Wannan saukin farashi ya biyo bayan sabon girbi da kuma matakan gwamnati na sauƙaƙa harajin shigo da kaya.

Advertisement

Hukumar Kididdiga ta Ƙasa (NBS) ta bayyana cewa hauhawar farashin kayayyaki ya sauka daga kashi 24.23 cikin ɗari a watan Maris zuwa kashi 23.71 cikin ɗari a watan Afrilu 2025.

Rukunin jami’o’i na MAAUN ta ƙulla yarjejeniyar koyar da Turanci, musayar ɗalibai da Kwalejin Seneca a Canada

Sai dai duk da wannan rahoto, masu gidajen cin abinci da kuma  unguwanni ba su rage kuɗin abincin da suke siyarwa ba.

Advertisement

A cewar jama’a, abincin da ake ci a kasuwanni da gidajen cin abinci har yanzu yana kan tsada, lamarin da ya nuna bambanci tsakanin rahoton gwamnati da abin da ake gani a zahiri.

Masanin tattalin arziki, Abdulsalam Isiya, ya bayyana cewa dalilin hakan shi ne matsalar farashi.

Advertisement

A cewarsa, ’yan kasuwa kan fi son su siyar da tsohon kaya kafin su rage farashin sabon kaya. Shi ma Dr. Junaidu Salih na Jami’ar Ahmadu Bello Zariya ya ce kudaden sarrafawa da ribar kasuwanci suna hana masu abinci rage farashi duk da cewa kayayyaki sun yi sauƙi a kasuwanni.

Wata mai gidan cin abinci a Zariya, Larai John, ta ce abincin da take siyarwa ba ya ta’allaka ne kawai da farashin kayan kasuwa ba. Ta ce tana ƙara kuɗin gudanarwa da ingancin abinci a cikin kudin cin abinci. Haka kuma, wata mai sayar da kayan abinci a kasuwar Samaru, Esther Auta, ta ce kuɗin sufuri da ingancin kayan abinci suna da tasiri wajen ƙayyade farashin, abin da ya sa bambanci ya kasance tsakanin dillalan kasuwa da masu gidajen abinci.

Advertisement

Duk da haka, masana sun ce saukin farashin zai iya bayyana kai tsaye ne idan sabon girbi ya cika kasuwanni tare da saukar kuɗin sufuri da rage matsalolin sarrafawa. A halin yanzu, rahotanni sun tabbatar da saukin farashin kayan abinci, amma jama’a na cigaba da korafi cewa wannan sauki bai bayyana a abincin da ake ci a kasuwanni da gidajen abinci ba.

 

Advertisement

 

 

Advertisement

NIGERIAN TRACKER

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending